Laugh Out Loud

These Hausa Stories are updated periodically and are not written by Bangeez.

Photo Credit: Hausa Writers Series

MAI LABARAN ZAI GUDU

Wani Danfillo ne ya ajiye rediyonsa ya tafi daji kiwo tsawon watanni bai dawo ba, har bera ya huda rediyon ya shiga ciki ya lalata wayoyin cikin rediyon, da ya ga ba a damu da ita ba, sai ya sami mazauni a ciki ya zauna.
Ranar da Danfillo ya dawo gida, ya dauki rediyo ya kunna, rediyo ta ki yi, don haka ya dauketa, ya kai ta wajen mai gyara.

Mai gyara yana kwance rediyo domin gyarawa sai ga wani dirkeken bera ya fito da gudu yana neman matsera, Danfillo na ganin haka ya yi zumbur ya bi beran nan yana ihu yana cewa.
“Jama’a a taimaka a taro min shi mai labaran ne zai gudu, a tare min mai labarai zai gudu.”

Photo Credit: Mujallar Marubuta

SANYI NE

Gajeren Labari
(c) Kabiru Yusuf Fagge (anka)

Wani mahaukaci ya zo wucewa ta bakin Kasuwar Sabongari, kawai sai ya ji wani mai sayar da maganin gargajiya yana talla, mahaukaci ya tsaya cike da mamaki yana kallo tare da sauraron mai maganin nan kunne bude, bakin wangame a lokaci guda kuma ido tarwas.
Shi kuwa mai magani, bai san me ke gudana ba, yana ta tallansa bilhakki:
“Mayawuya, sanyi ne,
Radadin mukamuki, sanyi ne,
Makaki da zogi, sanyi ne,
Kora ta dami yaro, sanyi ne,
Amosani ka, sanyi ne,
Ciwon baya, sanyi ne,
Yawan atishawa, sanyi ne,
Ido yana wani duru-duru, sanyi ne,
Yawan hamma, sanyi ne,
Jiri-jiri, sanyi ne,
Yawan tusa, sanyi ne,
Sanyi ne, sanyi ne, sanyi ne……
Wannan talla ta ishi mahaukacin nan, kawai sai ya sudada ta bayan mai tallar maganin nan, ya zage tun karfinsa ya sharara masa mari, ji kake “Kauuuuuuu!”
Mai tallan magani ya yi saurin kallon mahaukaci, tare da rike kumatunsa wanda ba tare da bata lokaci ba, tuni har ya kumbura, bai iya cewa komai ba face fashewa da kuka da ya yi.
Wasu mutane da ke gefe ne suka iya magana, suka daka wa mahaukacin nan tsawo, suna cewa “Kai me ya sa ka mare shi?”
Mahaukacin nan ya yi dariya yana kallonsu, ya ce, “SANYI NE!!”
Mutanen suka kwashe da dariya, suka jinjina kai, suna fadin “E, lallai kam sanyi ne.”

Photo credit: Hausa Writers Series

KU TAYA SHI

Wani manomi ne mai suna Sule Kankan, ya sabi fartanyarsa ya tafi gona don yin noma, yana zuwa, ya tattare hannun riga zai fara yin noma, sai ya ji kamar daga sama an ce.
“KU TAYA SHI!”

Ya bude baki yana mamaki, kafin ya juyo da hankalinsa, kawai sai ya ga an nome masa gonar. Ya tsaya yana mamaki, amma cikin jin dadi.

Washegari Sule Kankan ya dawo gona zai yi shuka, nan ma yana shirin fara aiki, sai ya ji an ce “KU TAYA SHI!” Take ya ga har an gama yi masa shuka.
Sule ya cika kuma ya ci gaba da rayuwa cikin mamaki, har zuwa lokacin yin huda, Sule ya nufi gona don yin huda, nan ma kafin ya fara aiki sai ya ji an ce “KU TAYA SHI!” Sule yana tsaye aka yi masa huda aka gama.

Abin mamaki har zuwa lokacin cire amfanin gona don kaiwa gida, Sule ya zo don tattare amfanin gona ya kai gida, kawai sai ya ji an ce “KU TAYA SHI!”
Hankalin Sule ya tashi lokacin da ya riski an kwashe amfanin gonar gaba, ai take ya fashe da kuka yana fadin, “DON ALLAH KAR KU TAYA NI!”

Photo Credit: Hausa Writers Series

JIBRILU NE DAGA SAMA

Wani yaro ne mai suna Jibrilu Musa aka kai shi makarantar kwana ta boarding. Sannan kuma a dakin kwanan daliban (hostel) da aka kai shi gadon da ya samu hawa hudu ne, kuma aka bashi hawan karshe.

Wata rana can tsakar dare suna barci, sai fitsari ya kama Jibrilu ya rasa yadda zai yi, sai ya fara ihu yana kuka, hakan ya sa wasu da yawa daga cikin dakin suka tashi.

Sai shugaban dakin ya motsa ya daga murya ya ce, “Wai wane ne nan yake yi mana kuka?”

Jin haka ya sa Jibrilu ya yi farat cikin muryar kuka ya ce “Wallahi Jibrilu ne daga sama ta hudu…”

Dalibai da shugaban daki suna jin haka sai suka ce kafa me na ci ban baki ba, sai gudu radadada! Dadada!!